1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgiza kasa a Phillipines

February 18, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7c

Rahotani daga kasar Phillipines sun ambata cewar wata mumunar girgiza kasa ta wakana, a wasu garuruwa dake tsakiyar kasar.

Wannan girgiza kasa,ta yi sanadiyar mutuwar mutane 109 , sannan, ya zuwa yanzu, akwai mutane a kalla dabu daya da dari 5, da su ka yi kasa ko bisa.

Ma´aikatan bada agaji na ci gaba, da zakulo gawwawaki.

Saidai su na fuskanatr matsaloli a dalili da ruwan sama da ke ciki gaba da sauka, a yankin da abun ya faru.

Tun daga farkon makon da mu ke ciki, ruwan sama kamar da bakin kwarya, sun yi sanadiyar mutuwar mutane 20.

Hukumomin bada agaji, sun kwashe mazauna garuruwa, masu makwabta da wurin hatsarin.

Wanda su ka ganewa idon su yadda bila´in ya wakana sun shaida cewar daga garuruwa 375, da massifar ta fadawa, gidaje yan kwarori kadai su ka rage.

Tunni dai kungiyoyin kasa da kasa, da kasashe masu hannu da shuni, sun bayyana aika tawagogin agaji, da kuma tallafi na kudade da kayan aiki.