Girgiza kasa a kasar Papua New Guinea | Labarai | DW | 11.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgiza kasa a kasar Papua New Guinea

Wata girgizar kasa da karfin ta ya kai awo 6.8 a ma´aunin Richter ta auku a kusa da gabar teku a gabashin kasar Papua New Guinea. Kamar yadda cibiyar nazarin bala´o´in girgizar kasa a Hongkong ta nunar girgizar kasar wadda ta auku da misalin karfe biyu da rabi agogon GMT, ta fi karfi ne a wani yanki mai nisan kilomita 270 a can cikin teku kudu da tsibirin New Birtaniya. Kawo yanzu dai ba´a san irin barna ko salawantar rai da girgizar kasar ta haddasa ba. A cikin watan yuli shekarar 1998 sama da mutane dubu 2 suka rasu a kasar ta Papua New Guinea sakamakon wata girgizar kasa da ta auku a karkashin teku.