Girgiza ƙasa a Indonesia | Labarai | DW | 06.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgiza ƙasa a Indonesia

Wata mummunar girgiza ƙasa, ta sake rutsawa da Indonesia, da sahiyar yau talata.

An ji wannan girgiza har Singapour da ke tazara kilomita 430, da yankin Sumatra na Indonesia, inda ya abun ya faru.

Hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia, mai kulla da ƙananan yara, ta bayyana cewar a ƙalla mutane fiye da 80 su ka rasa rayuka, a cikin wannan bila´i, wanda bugu da ƙari yayi sanadiyar assara dukiya mai yawa a Sumatara.

Ƙurrarun masana masana,ta fannin borin ƙarshen ƙasa, sun ce girgiza ƙasar ta kai mizanin awo kussan 6 ,na ma´aunin rishita.

Indonesia, na ɗaya daga ƙashen dunia, da su ka fi fama da ire-iren wannan bila´o i ,daga indallahi.