1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgiza ƙasa a Indonesia

May 30, 2006
https://p.dw.com/p/BuwD

Ƙasashe da ƙungiyoyin bada agaji na dunia, na ci gaba da kai taimako ga al´umomin Indonesia da bala´in girgizar ƙasa ya rutsa da su.

Har yanzu, a na ci gaba da gano ƙarin mutanen da su ka rasa rayuka a cikin wannan bila´i.

Alƙalluman baya bayan nan, da gwamnati Jakarta ta bayar, sun ce rayuka a ƙalla 5.400, su ka salwanta a cikin wannan girgiza ƙasa.

Dubunan jama´a, da su ka rasa matusugunnai, sun share dare na 3 ,a cikin yanayi mai ban tausayi.

Assibitocin ƙasar sun cika maƙil, sannan ga babu issassun ma´aikata da magungunna.

Majalisar Ɗinkin Dunia, ta yi kira ga ƙasashe masu hannu da shuni, su girka manyan assibitoci 3, cikin gaggawa, da kuma taimakon maggunguna.

Ƙarin al´ajabi, a yanzu haka, a na cikin zullumin abukuwar wata sabuwar girgiza ƙasa.