Gina gabashin jamus zai cigaba da zama fifikon gwamnati | Labarai | DW | 03.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gina gabashin jamus zai cigaba da zama fifikon gwamnati

Shekaru 17 bayan sake hadewar gabashi da yammacin tarayyar jamus,har yanzu gwamnati na cigaba da bawa yankin gabashin kasar fifiko wajen gininta.Shugabar gwamnati Angeka Merkel ta sanar da hakan yau ,bayan kammala adu’oi na musamman da aka shirya domin bukin wannan rana a wata majamia dake yankin arewa maso gabashin Jamus.Merkel tace har yanzu Gabashin kasar na bukatar gyare gyaren kayayyakin more rayuwa,domin inganta ta kamar yankin yammaci.Shugabar gwamatin wadda ta girma a yankin gabashin kasar tace,koda yake an cimma nasara a wasu bangarorin,gwamnatin ta zata cigaba da sanya fifiko wajen cigaba da ginin yankin.Wannan Addu’a ta yau,wadda tasamu halartan shugaban kasa Hoest Koeler,na mai kasancewa daya daga cikin muhimman bukukuwa da aka gudanar a fadin tarayyar jamus.