Giletta Mouyabi mai taimaka wa mata a fannin ilimin kwamfuta | Sauyi a Afirka | DW | 11.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Giletta Mouyabi mai taimaka wa mata a fannin ilimin kwamfuta

Kungiyar ilimantar da mata a Benin ta dukufa wajen sauya wa matan kasar tunani don ganin sun rungumi amfani da wayoyin salula da na'urar kwamfuta.

A Jamhuriyar Benin, wata mata mai suna Giletta Mouyabi da ke aiki a sashen fasahar sadarwar zamani tsawon shekaru, yanzu ta dukufa don ganin mata a kasar sun rungumi amfani da wayoyin salula ko kuma ma amfani da na'ura mai kwakwalwa wato kwamfuta. Kamfaninta na taimakawa wajen ba da tallafi kuma na taimaka wa masu kananan masana'antu karkashin jagorancin wata kungiya mai sunan "World Women Education" wato Tarbiyyar Matan Duniya.

Suna son ba da muhimmanci ne sosai bisa tsarin yada labarai na zamani ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa. Tarin matan da ke sauraron Giletta Mouyabi, suna da burin samun nasara, da kuma buda wani sabon babi na aiki. Son samun kwarewa ga amfani da kwamfuta abu ne mai kyau, amma kuma yanzu ne aka fara, inji ta.

"Ya na da kyau mutun ya yi tunanin da ya dace wajan cimma burin da ya sama gaba."

Share fagen samun mata jagorori na gari

A wani mataki na karfafa wannan tsari, tana ganawa ne da mata sau daya ko sau biyu a wata.

Mobiltelefon

Sanin makamar amfani da wayar salula na cikin abubuwan da ake koya wa matan

Tana basu shawarwari tare da kuzari. Tare da wannan kungiya tata mai suna Tarbiyyar Matan Duniya, tana da burin horas da mata don samun mata jagorori na gobe a fannin amfani da na'ura mai kwakwalwa.

"Wannan fanni ne da akasarin 'yan mata ba su cika damuwa da shi ba. Akwai wasu 'yan kwarori da suka fara samun horon, an hada su gaba daya suna musayar abin da suka koya da sauran 'yan mata. Saboda su taimaka, su zama jagororin wannan fannin nan gaba. Nasarar hakan zai taimaka wajen ci-gaban kasarsu."

Giletta Mouyabi na jagorancin wani sabon tsari da aka wa suna biya kai tsaye a kasar Benin. Wani tsari ne na intanet da ke nuna hanyoyi da dama na biyan kudade ta intanet. Duk da cewa tana a matsayin mai hannun jari cikin wannan kamfani, amma kuma tana ba da shawarwari ne bisa hanyoyin da suka kamata a aiwatar da wannan tsari, don gamsar da abokan cinikayya. Wannan kamfani na hulda ne da kamfanoni da dama na kasa da kasa da suka hada da na kasar ta Benin, da Afirka ta Kudu, Burkina Faso, Côte-d'Ivoire da kuma Senegal.

"Za a yada wannan tsari ne a dukannin sassa dabam-dabam kamar na bayar da ilimi, ko kuma kiwon lafiya domin duk wannan tsari ne da gwamnati ita kadai ba za ta iya aiwatarwa ba. Don haka muke kirkiro da kamfanoni, muna kuma ba da namu tallafi, ta yadda za su iya gudanar da ayyuka domin tallafa wa gwamnati ta wani bangare."

Ababan more rayuwa kadai ba za su wadatar ba

Cotonou Benin

Manyan gadoji a Cotonou babban birnin Benin

Kasar Benin dai na daya daga cikin kasashen Yammacin Afirka, kuma daya daga cikin kasashe matalauta a duniya. An kafa tsari da dama na samar da ruwan sha mai tsabta, da kuma wutar lantarki. Sai dai wadannan kadai ba za su wadatar da kasar ba, a cewar Giletta Mouyabi.

"E za ka iya ci-gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka kamar na ruwa da wutar lantarki. Wannan ayyukan bukatarsu na karuwa. Amma dai kar su hana wa Afirka tunanin wasu bangarorin raya kasa da ake da su a duniya. Don haka ana bukatar tunanin amfani da intanet da sauran fasahohin sadarwar zamani."

Giletta Mouyabi ta ce kasarta na samun bunkasa. Hasali ma alkaluman da Bankin Duniya ya fitar, ya nuna tattalin arzikin Benin a matsayi na 16 a jerin kasashe makobta kamar su Kamaru da Senegal.

Sauti da bidiyo akan labarin