1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gidan tarihi na Birtaniya ya karrama Salah

Gazali Abdou Tasawa
May 17, 2018

Shahararren gidan ajiyar kayan tarihi na Birtaniya da ke a birnin London ya sanya takalamin kwallon kafa na Mohamed Salah a jerin manyan kayan tarihin kasar Masar

https://p.dw.com/p/2xuG7
West Bromwich Albion - FC Liverpool Mohamed Salah
Hoto: picture-alliance /dpa/PA Wire/N. French

Gidan ajiyar kayan tarihi nan na kasar Birtaniya a birnin London ya karba tare da jera takalamin kwallon kafa na Mohamed Salah shahararren dan wasan kwallon kafar kasar Masar, a cikin jerin manyan kayayyakin tarihin kasar ta Masar da ake ajiye da su a wannan gidan kayan tarihi.

Kamfanin da ke yi wa Mohamed Salah takalmin da yake taka leda da su a gasar ta Primiya Lig ne ya bai wa gidan ajiyar kayan tarihin na Birtaniya kyautar takalmin kwallon kafar jarimin, da nufin karrama shi a sakamakon bajintar da ya nuna ta kasancewa dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a gasar Primiya ta bana da kwallaye 32 a wasanni 38. 

Babban jami'in da ke kula da gidan ajiyar kayan tarihin Neal Spencer ya bayyana gamsuwarsa da karbar takalmin kwallon kafar dan wasan na Masar  wanda ya ce zai taimaka wa wani shiri da suke da shi na kaddamar da wani tsari musamman na karbar kayayyakin tarihin kasar Masar na karni na 20 da na 21.