Gidan Burj Khalifa ne mafi tsawo a Duniya | Amsoshin takardunku | DW | 24.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Gidan Burj Khalifa ne mafi tsawo a Duniya

An fara wannan gini ne a ranar 21 ga watan Satumban shekara ta 2004.

default

Gidan Burj Khalifa a Dubai

Tarihin ginin da ya fi kowanne tsawo a Duniya wanda ke birnin Dubai na haɗaɗɗiyar daular Larabawa.

Shi dai wannan gini shine wanda ake kira Burj Khalifa Tower. An kuma fara gina shi ne a ranar 21 ga watan Satumban shekara ta 2004. Kuma an kammala ginin ne a ranar 1 ga watan Oktoban 2009, tare kuma da ƙaddamar da shi a ranar 4 ga watan Janairun 2010.

Wannan gini wanda gwamnatin Dubai ta gina wani kanfanin ƙasar Koriya ta Kudu da ake kira Samsung C&T ne ya gina shi. A watan Junin shekarar 2010 nan da muke ciki ginin mai suna Burj Khalifa ya samu kyautar yabo na kasancewa ginin da ya fi kowanne tsawo a gabas ta tsakiya da kuma Afirka.

Bincike dai ya nuna cewar an kashe zunzurutun kuɗi har Dalar Amirka miliyan dubu ɗari ɗaya da rabi wajen gina shi. An kuma sanyawa ginin sunan shugaban haɗaɗɗiyar daular larabawan ne Khalifa bin Zayed Al Nahyan da akewa laƙani da Burj Khalifa saboda gudumawar da ya bayar wajen gudanar da ginin.

Sai dai Kafin gina Burj Khalifa a matsayin ginin da yafi tsawo a duniya akwai wasu gine gine dake riƙe da wannan kanbu da suka haɗa da Husumiyan gidan Talabijin dake Jihar North Dakota a Amirka da kuma wani a birnin Warsaw na Poland.

Bayan waɗannan akwai ginin Taipei 101 da ke ƙasar Taiwan da kuma Cibiyar kasuwanci ta birnin Shanghai a China. Sai dai kuma duk da cewar ginin na Burj Khalifa shine yafi kowanne tsawo.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Balaraba Abbas