Gidajen Ajiya nawa ƙasar Jamus ta mallaka | Amsoshin takardunku | DW | 18.02.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Gidajen Ajiya nawa ƙasar Jamus ta mallaka

Bayani game da yawan Gidajen Ajiyar da ƙasar Jamus ta mallaka

default

Wani Gidan Ajiya a birnin Koblenz

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Sa'adu Ayuba dake birnin Agadas a jamhuriyar Niger. Malamin cewa ya yi don Allah filin amsoshin takardunku, ina so ne ku sanar da ni yawan Gidajen Ajiya da ƙasar Jamus take dasu na ajiyar rubutattun kayan tarihi da kuma sauran kayayyaki irin su Hotuna da tsaffin Fina-finai da taswirori da dai sauran su.

Amsa: To Mallam Sa'idu Ayuba batun yawan Gidajen Ajiyar da ƙasar Jamus ta mallaka abu ne mai wuyar ƙididdiguwa, domin kusan dukkanin biranen ƙasar Jamus suna Gidajen ajiya da yawan gaske. To amma babbar cibiyar adana kayayyaki da bayanai ta gwamnatin tarayyar Jamus tana birnin Koblenz ne, kuma tana tattare da bayanai da dama kamar hotuna, da zane-zanen taswira, da faya-fayen Sinima, da dai wasu kayan tarihi.


Babbar Cibiyar na da rassa guda biyar waɗanda ke ƙunshe da bayanan binciken da aka gudanar kan muhimman aikace-aikace na tsohuwar daular Jamus wato (Reich), wadda tai zamaninta kafin yaƙin duniya na na daya. Har ila yau kuma akwai bayanai na ayyukan rundunar sojin Jamus mai suna rundunar (Reichswehr ), wadda ta yi zamaninta tun daga shekarar 1919 zuwa 1935, Sai kuma bayanan abubuwan da suka gudana a zamanin gwamnatin (Wehrmact ) wato tsohuwar gwamnatin Hitlar. Akwai kuma bayanai na tsohuwar gwamnatin Jamus ta Yamma tun daga 1945 zuwa 1949.

Ba'ada bayan haka wannan cibiyar tanadin kayan ajiya ta Jamus tana da cikakkun bayanai game da wallafe-wallafe dake ƙunshe da bayanai daban-daban, akwai kuma mujallu, da ƙasidu da hotunnan ‘yan Siyasa dake sanar da tallan ‘yan takarar siyasa na wancan zamani.

Wata Cibiyar dake da irin waɗɗan nan muhimman bayanan kuma ita ce wadda ke birnin Barlin. Cibiyar ta Barlin tana da bayanan abubuwa da jam'iyyar NAZI da kuma ƙungiyoyin ‘yan Nazi, kafin daga baya gwamnatin tarayyar Jamus ta mayar da su cibiyar tara kayan tarihi na gwamnati a watan Yuli na 1994.

Dukkanin bayanan kayan ajiya muddin dai hukumar binciken cikin gida ce ta samar da su, to a tsarin doka, jama'a na iya dubawa don yin amfani da su. A halin yanzu, hukumar tarayyar ce ta Jamus ke samar da irin waɗannan bayanai daga babban ofishin tanadin kayan tarihi na Jamus dake Barlin, kuma yana da rassa 14, a ɗaukacin gabashin Jamus.