Giɓin kasafin kuɗi a Tarayyar Jamus | Siyasa | DW | 25.08.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Giɓin kasafin kuɗi a Tarayyar Jamus

Matsalar tattalin arziki na cigaba da shafar ƙasashen Duniya

default

Tashar jiragen Ruwa masu jigilar Kaya na Hamburgh

Matsalolin tattalin arziki da Duniya ke fama dashi ya jefa kasafin kudin tarayyara Jamus cikin watanni shidan farko cikin hali mawuyaci.

Ofishin ƙididdiga na Tarayyar Jamus da ke birnin Wiesbadenya ruwaito cewar, hakan ya danganta ne da koma bayan kudaɗen shiga da kuma irin ɗumbin kuɗin da gwamnati ta kashe wajen cike giɓi, wanda yawansa yakai kimanin Euro Biliyan 17.3. A farkon watanni shidan shekarar 2008 data gabata dai, an samu karuwan kuɗaɗen shiga na wajen sama da biliyan bakwai.

Hanyoyi biyu da za a iya bayyana kasafin kuɗin tarayya, jihohi da na ƙananan hukumomi shi ne, Faɗuwar kuɗaɗen haraji, da kuma tashin kuɗaɗen kashe-kashe akan ayyuka, inji Farfesa Winfried Fuest, dake cibiyar kula da harkokin tattali, kasafin kudi da kashe kashen gwamnati da haraji.

Prof. Dr. Winfried Fuest

Prof. Dr. Winfried Fuest.

"ya ce a ɓangaren kuɗaɗen shiga, akwai ƙaruwa da ake samu ta fannin kayayyakin da ake juyawa, alal misali kamar kashi 40 daga cikin 100. Ayayinda ake rage yawan kuɗaɗen albashi, saboda raguwar lokutan aiki. A ɓangaren kuɗaɗen da ake kashewa kuwa, aiki na gajeren lokaci bawai yana cin kuɗi mai yawa kaɗai ba, amma harma da lokacin da za a ɗauka ana tattauna yarjejeniyar data shafi ma'akata, kamar girmar da yara. An sanya kasafin kuɗin ta fannoni biyu wanda a wasu lokuta, yakan kasance abun takaici"

A takaice, dole a cigaba da kasancewa da babban giɓi a kasafin kuɗin gwamnati, dangane da ɗunbin makuddan kuɗaɗe da aka fidda domin farfaɗo da wasu hukumomi da Bankunan da ke neman durkushewa. Sai dai ba a cika ganin waɗannan matsalolin a cikin tsarin kasafin tarayya ba, kasancewar suna ɓoye amma a hukumance.

A yanzu haka dai sakamakon matsin lamba daga ɓangaren Faransa, Ƙungiyar Tarayyar Turai ta daina sanya kuɗaɗen farfaɗo da tattalin arziki a matsayin giɓin kasafi.

Kididdigan Tarayyar Turai dai na nuni dacewar, Jamus ta cimma sharaɗin yarjejeniyar Maastrich da giɓin kashi 1.5 na jimlar kayayyakin da ƙasa ke samarwa. Farfesa Winfried Fuest yayi karin haske...

Symbolbild von Klimaschutz in Zeiten der Finanzkrise

Sauyin yanayi da matsalolin tattali.

"Yace bugu da kari akwai kuma ka'idoji da aka gindaya. Alal misali, za a kawar da shi ne kawai a bayan watannin shida na farkon shekara. Duk dacewar an rigaya an gabatar da aiki a akansu ko kuma akasin hakan, sa'annan kuma daura da komai halin da ake ciki na dangane da giɓi"

Daura da komai dai ana jiran yadda zata kasance a karshe. A tsawon shekarar, gwamnatin tarayya na kyautata zaton samun giɓi na kashi 4 daga cikin 100 na adaddin tattalin arzikinta. Kana a shekara mai zuwa tana kyautata zaton samun giɓin kashi shida daga cikin 100, wanda ya ninka adadin da akan bari a yanayi na daidaituwar tattalin arziki.

Mawallafiya: Zainab Mohammad

Edita: Mohammad Nasir Awal