Ghana ta lashe wasan ta da ta yi da Czeck da ci biyu ba ko daya | Labarai | DW | 17.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ghana ta lashe wasan ta da ta yi da Czeck da ci biyu ba ko daya

A gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da ake yi yanzu haka a nan Jamus, Ghana ta zama kasar Afirka ta farko da ta yi nasara a gasar ta bana. A wani wasa mai kayatarwa da suka kammala dazu dazun nan a birnin Kwalan kungiyar kwallon kafa ta Black Stars ta sharewa ´yan Afirka hawaye, inda ta lashe takwararta ta janhuriyar Czeck da ci biyu da nema. Da kusan minti biyu da fara wasan dan kai hari na Ghana wato Gyan Asamoah ya saka kwallo a ragar Czeck yayin da Sulley Muntari ya ci kwallo na biyu bayan mintuna 82 da fara wasa. Kafin haka dan wasan na Ghana wato Asamoah ya yar da bugun da ga kai sai mai tsaron gida wato penalty. A wasan da aka yi yau da rana Portugal ta lashe Iran da ci biyu da nema. In an jima kadan Italiya zata kara da Amirka.