Ghana ta hana kamun kifi a fadin kasar. | Labarai | DW | 07.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ghana ta hana kamun kifi a fadin kasar.

Hukumomi a kasar Ghana sun hana kafun kifi a fadin kasar na tsawon watanni biyu a wani mataki na kare kifayen daga karewa da kuma bada damar hayayyafar kifayen domin bunkasa wadatar su.

Kimanin kashi 10 cikin dari na al'ummar Ghana sun dogara ne ga kamun kifi a harkokin su na rayuwar yau da kullum.

Ggwamnatin ta ce kifayen na iya karewa idan ba'a dauki matakin hana yin su din musamman a manyan kogunan kasar ba.

Sai dai kuma masu harkar sana'ar kifin sun ce matakin bai yi musu dadi ba a cewar Naa Quartey wata mai sanar kifin. 

"Za mu je mu zauna a gida a na tsawon watanni biyu, babu shakka wannan zai shafi rayuwar mu. Kowa na juyayin wannan al'amari, musamman na'urar sanyi da muke haya domin zuba kifi, ko ka ajiye kifi ko baka ajiye ba sai ka biya, a saboda haka wannan hasara ce a gare mu"

A baya bayan nan dai masunta a kasar ta Ghana sun koka cewa basa samun kifi sosai duk da tsawon lokaci da suke dauka bayan shimfuda fatsa a kogi, lamarin da aka dora alhakinsa akan hanyoyi mara sa inganci na kamun kifin wanda baya barin ko da 'ya'yan kifayen ne.