Ghana ta cika shekaru 60 da samun ′yancin kai | BATUTUWA | DW | 06.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Ghana ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai

Ranar Litinin 6 ga watan Maris rana ce da kasar Ghana ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai daga Turawan Ingila. Kuma sunan "Kwame Nkrumah" na ci gaba da daukar hankali saboda gudunmawar da ya bayar.

Kwame Nkrumah da sarauniyar Ingila

Kwame Nkrumah da sarauniya Elizabeth ta Ingila

 

Kwame Nkrumah, tsohon Firaminista da Shugaban kasa shi ne ya jagoranci Ghana zuwa samun 'yanci. A wancan lokacin ya tsaya a gaban 'yan kasar ya kuma bayyana cewa Ghana ta sami 'yanci ne na har abada. A shekarar farko da samun 'yancin kai, gwamnatin Kwame Nkrumah ta zo da tsare-tsaren dora kasar bisa turbar samun ci gaba da bunkasar masana'antu, sabanin yadda kasar ke dogaro kacokan kan harkokin noma ba.

Aikin madatsar ruwa na Volta River har yanzu na zama inda lantarki ke samuwa a kasar. Sai dai da dama cikin ayyukan da tsohon Shugaban ya dora kasar a kai, sun rushe saboda yawan cin bashi da cin hanci da rashawa gami da rashin iya gudanar da harkokin gwamnati daga wadanda suka karbi jagoranci a kasar.

Kwame Nkrumah

Kwame Nkrumah

Sai dai a zamanin tsohon Shugaba Nkruma an ga kokari na kama karya da mayar da kasar bisa tsarin bin jam'iyya daya tilo tare da bayyana kansa a matsayi na wanda zai mulki kasar Ghana har abada. Dubban 'yan kasar masu fada a ji sun yi kaura zuwa kasashen waje don neman mafaka kafin a shekarar 1966 lokacin da ya yi tafiya zuwa kasar China, sojoji suka hambarar da gwamnatinsa. Duk wadannan wasu abubuwa ne da matasan yanzu da dama ba su sani ba, a fadar Burkhardt Hellemann, na gidauniyar Konrad Adenauer mai fafutukar kare dimokuradiyya a ofishinsu da ke a Ghana.

''Ya ce har yanzu wannan suna na da muhimmanci a Ghana domin ya jagoranci samun 'yancin kasar ta Ghana, sai dai da yawa a kasar basu san yadda ya yi mulki ba a lokacin ya ke firaminista ko shugaban kasa''   

A ra'ayin Atsu Aryee, malami a jami'ar Ghana, tsohon Shugaban duk da irin cece-ku ce da ke a kansa ya taka muhimmiyar rawa ganin yadda a wasu kasashe a lokaci irin nasa aka rika samun masu son ballewa daga kasar duk da samun 'yancin kan kasa.

''Ina ganin tsarinsa na kishin kasa abu ne da ya yi tashe lokacin da ya ke mulki, wannan na tasiri a tasakanin 'yan kasa har yanzu  muna da kasa guda kuma kasa dole ta ci gaba da zama wuri guda''

Shagulgulan samun 'yanci a Ghana

Shagulgulan samun 'yanci a Ghana

Kwame Nkrumah dai sananne ba a nahiyar Afirka kadai ba, har ma da wasu kasashen duniya saboda fafutukarsu ta kishin Afirka. A shekara ta 2004, sunan Nkrumah ya zama na biyu bayan marigayi Nelson Mandela na kasar Afirka ta Kudu a nahiyar, a fadar mujallar  "New African",  Tsarinsu na  kishin kasa da ma na Afirka duk da kokarin wasu tsirarun 'yan fafutuka a wannan zamani ba a cika jin duriyarsu ba a fadar Farfesa Falola na sashin nazarin Afirka a jami'ar Texas. A kasar Ghana bayan shekaru jam'iyyar CPP ta su Kwame Nkrumah ba ta taka rawa sosai a siyasar kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin