Ghana: Mutane 22 sun mutu wajen ginar zinari
July 7, 2017Talla
Mahakar mai zurfin mita 80 wacce aka daina aiki da ita wadda kuma gwamntin ta haramta a farkon wannan shekara ta rubta da masu ginan zinarin a ranar Lahadin da ta gabata. Ghana dai ita ce kasa ta biyu a Afirka bayan Afirka ta Kudu wadda da ke da arzikin karfen zinari, sai dai a karo da dama a kan samu irin wannan hadari.