Ghana: Al′umma ta soma kada kuri′a | Siyasa | DW | 06.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ghana: Al'umma ta soma kada kuri'a

Sama da mutane miliyan 15 za su kada kuri'a a zaben na shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki.

Shekaru hudu da suka gabata man fetur ya mamaye yakin neman zabe amma yanzu ba kasafai ake ambato shi ba. Ishmael Edjekumhene daraktan kamfanin fasaha na Kite, da ke zama wata cibiyar binciken kimiya da makamashi da ke birnin Kumasi ga yadda yakekallon wannan muhawara:

"Gwamnati ta ce wani bangare na ribar da ake samu ya shiga cikin tsarin inshoran kiwon lafiya. Babbar jam'iyyar adawa mai muhimmanci a daya hannun, tana bukatar a yi amfanin da kudaden man fetur wajen gina kasa. Akwai lokuta kadan a gaskiya da ake tattauna man fetur."

A 'yan shekarun da suka gabata lamarin ya sha banban. Gano man fetur a shekara ta 2007 ya zama wani babban bangaren abin da ake tattaunawa dauke da fata. Jerry Sam da ke zama daraktan wani shiri na Pen Plus Bytes, kungiyar da ke taimakon 'yan jarida bincike kan bangaren man fetur domin tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin kungiyoyi masu zaman kansu, ya yi karin haske:

 

"Muna jagorancin tattaunawa da kungiyoyi masu zaman kansu, domin tabbatar da mutane sun fahimci bangaren. Ya dace su tambayi 'yan siyasa, misali idan suka ce: Mun zuba kudaden man fetur a aikin gona. Me suke nufi da haka? Kashi nawa aka zuba? Za mu yi haka saboda man fetur da gas sun zama manyan abubuwa da ake mayar da hankali a kansu a zaben."

 

Ganin cewa man fetur bai zama abin da ya mamaye komai ba a zaben na bana akwai dalilin haka. Misali wata cibiyar kula da harkokin siyasa ta ce saboda rashin yawa da kuma cewa man zai kara raguwa a shekara ta 2018. Ishmael Edjekumhene ya kwatanta lamarin da zinaren da kasar ta taba ganowa:

 

"Idan mutum ya duba tasirin tattalin arziki, babu yawa sosai. Mafita tana da sauki, a duba inganci a fayyace, babu kayayyakin da muke sarrafawa da suke da tasiri. Gagarumi shi ne na shekara ta 2014 da kimanin kashi 10 cikin 100."

 

Gwamnati ta yi fata bangaren man ya samar da dubban ayyuka. Amma wani rahoton Bankin Duniya ya ce daya cikin biyu na matasan Ghana ba su da wani karkarfan aikin yi, kuma zai yi wuya bangaren man fetur ya zama wata hanyar samar da aiki a kasar ta Ghana da ke yankin yammacin Afirka.

Sauti da bidiyo akan labarin