Germanwings: Za a kai ƙara a gaban wata kotu a Amirka | Labarai | DW | 13.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Germanwings: Za a kai ƙara a gaban wata kotu a Amirka

Wasu daga cikin Iyalen mutanen nan,waɗanda haɗarin jirgin saman kamfanin sufirin jiragen sama na Jamus Germanwings ya rutsa da yan uwansu a shekara bara sun ce za su kai makarantar da matuƙin da ya yi karatu ƙara.

Iyalen un ce za su kai makarantar da matukin jirgin Andreas Lubitz ya yi karatu inda ya samu horo daga shekara ta 2010 zuwa ta 2011 ƙara a gaban wata kotu da ke a Amirka.
Makarantar ta horas da matuƙa jirgin sama mai sunan ATCA da ke a Arizona a kudu maso yammacin Amirka.Iyalen fasinjan da suka mutu na zarginta da nuna sakaci, wajen karɓar dalibin duk kuwa da cewar a cikin takardunsa na shaida na kiwon lafiya an nuna cewar a baya ya fi fama da tabin hankali.

A cikin watan Maris na shekara bara marigayi Lubitz ya faɗi da jirgin saman na kamfanin na Germanwings da ke ɗauke da fasinja 149 a cikin tsaunikan Faransa wanda daga cikinsu babu wanda ya fita har shi.