Georges Bush ya ɗura ɗamarar yaƙi da baƙin haure | Labarai | DW | 16.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Georges Bush ya ɗura ɗamarar yaƙi da baƙin haure

Shugaba Georges na Bush na Amurika, ya bayyana ɗaukar matakai ƙwaƙwara domin yaƙi da baƙin haure da ke ci gaba da kwarara zuwa Amurika mussamman daga ƙasar Mexique.

A dangane da hakan Bush ya yanke shawara aika jami´an tsaro dubu 6, a iyaka tsakanin Mexique da Amurika, domin sa iddo, ga kwaraar bakin haure.

A nasu ɓangaren yan majalisar dattawan Amurika mafi rinjaye, sun bada goyan baya ga wannan mataki, saidai ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama, na cikin zullumin anfani da damar, domin tozarta jama´a.