1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Georges Bush ya ɗura ɗamarar yaƙi da baƙin haure

May 16, 2006
https://p.dw.com/p/Buy9

Shugaba Georges na Bush na Amurika, ya bayyana ɗaukar matakai ƙwaƙwara domin yaƙi da baƙin haure da ke ci gaba da kwarara zuwa Amurika mussamman daga ƙasar Mexique.

A dangane da hakan Bush ya yanke shawara aika jami´an tsaro dubu 6, a iyaka tsakanin Mexique da Amurika, domin sa iddo, ga kwaraar bakin haure.

A nasu ɓangaren yan majalisar dattawan Amurika mafi rinjaye, sun bada goyan baya ga wannan mataki, saidai ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama, na cikin zullumin anfani da damar, domin tozarta jama´a.