1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakilin Amurika a gabas ta tsakiya ya fara rangadi na biyu

Sadissou YahouzaFebruary 25, 2009

Wakilin Amurika a gabas ta tsakiya George Mitchell ya shiga rangadi na biyuz a yankin tun bayan da ya hau wannan muƙami.

https://p.dw.com/p/H19G
Ziyara G.Mitchell a gabas ta tsakiyaHoto: AP

A yau laraban nan ne wakilin musamman na Amurka akan Yankin Gabas ta Tsakiya George Mitchell ya fara ziyara karo na biyu ga wannan yanki a ƙoƙarin samar da kusantar juna tsakanin Isra'ila da Palasɗinawa. Tun a jiya talata Mitchell ya fara yada zango a London kafin ya zarce zuwa Turkiyya, Haɗɗaɗiyar Daular Larabawa, Masar, Isra'ila da yammacin kogin Jordan. Babban aikin da aka dora wa kwararren jami'in diplomasiyyar shi ne ya janyo hankalin sassan da basa ga maciji da juna a rikicin yankin domin su sake komawa kan teburin shawarwari. Ahmad Tijani Lawal na dauke da takaitaccen tarihinsa.

A ranar 22 ga watan janairun da ya wuce, sabon shugaban ƙasar Amurka Barack Obama, ya ba da sanarwar cewar zai yi iya ƙoƙarinsa wajen samar da wani dawwamammen zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasɗinawa. To sai dai kuma ga alamu yanayin da ake ciki a yanzun bai dace ba sakamakon yaƙin da aka gwabza a zirin Gaza. To sai dai kuma duk da haka, shugaban na Amurka na da niyyar bayyana fuskantar wata sabuwar alƙibla ga manufofinsa, inda ya nada George Mitchell a matsayin wakilinsa na musamman akan yankin gabas ta tsakiya tun a farkon wa'adin mulkinsa.

Obama ya ce:Gwamnati ta zata bi wata kakkarfar manufa ce dake da nufin samar da dawwamammen zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawa, a bangare guda, da kuma Isra'ilar da sauran makobtanta Larabawa a daya bangaren. Domin cimma wannan burin, ni da sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton, muka tambayi George Mitchell, ko yana sha'awar karɓar wakilici na musamman akan gabas ta tsakiya.

A nata ɓangaren sakatariyar harkokin wajen ta Amurka Hillary Clinton tayi bayani akan abin da ake sa ran gani daga seneta din mai shekaru 75 da haifuwa tana mai cewar:

Hillary Clinton ta ce:Zai jagoranci kokarinmu na sake farfado da shawarwarin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da makobtanta. Zai taimakemu wajen ƙirƙiro wasu manufofi masu ma'ana, waɗanda zasu tabbatar da tsaron Isra'ila bisa manufar kawo ƙarshen rikicin yankin gabas ta tsakiya, ta yadda watan-wata-rana za a wayi gari tare da kasashe biyu dake zama kafada-da-kafada da juna a cikin zaman lafiya da tsaro.

Duk da wannan dogon burin da aka saka a game da manzancin George Mitchell, amma fa jami'in, dan jam'iyyar democrats, fitacce ne a fannin shiga tsakani don neman zaman lafiya, musamman ma a matsaloli masu sarƙƙaƙiyar gaske. Kuma ba da wata-wata ba ya tofa albarkacin bakinsa a game da abin da yake gani zai taimaka a samu zaman lafiya. Dangane da Isra'ila cewa yayi:

Wajibi ne gwamnatin Isra'ila ta dakatar da matakanta na giggina matsugunan Yahudawa abin da ya hada har da bunƙasa waɗanda ke akwai.

A game da Palasɗinawa kuma jami'in diplomasiyyar cewa yayi:

Wajibi ne mahukuntan Palasɗinawa su dauki nagartattun matakai da zasu bayyanar a fili cewar ba zasu saduda da ta'addanci ba. Wajibi ne su yi bakin kokarinsu wajen murkushe duk wani mataki na ta'addanci da hukunta duk wanda ya keta haddi.

Shi dai George Mitchell mahaifiyarsa 'yar Lebanon ce ya kuma yi ƙaura zuwa Amurka yana da shekaru 18 na haifuwa. Watakila a sakamakon hakan larabawa zasu saurari ta bakinsa.