Gazawar Amirka a Iraki zai zama wani bala´i, inji Mista Gates | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gazawar Amirka a Iraki zai zama wani bala´i, inji Mista Gates

Sabon sakataren tsaron Amirka Robert Gates ya yi kashedi game da gazawar manufofin kasarsa dangane da Iraqi. A lokacin da ya ke jawabi bayan an rantsad da shi a birnin Washington, mista Gates ya ce rashin samun nasarar zai kasance wani bala´i. Gates wanda shi ne tsohon daraktan hukumar leken asirin Amirka CIA, shi ya gaji Donald Rumsfeld wanda ya yi murabus daga mukamin sakataren tsaro a cikin watan nuwamba. A wata sabuwa kuma wani nazari da ma´aikatar tsaron Amirka ta yi ya yi nuni da cewa halin tsaro a Iraqi ya kara tabarbarewa a cikin watannin baya bayan nan. Daga watan agusta zuwa watan nuwamba, yawan hare hare da ake kaiwa a Iraqin ya karu da misali kashi 20 cikin 100. Har yanzu kuwa dakarun Amirka da kawayensu aka fi kaiwa hari, inji rahoton na ma´aikatar tsaron ta Amirka.