1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matsin rayuwa a Gaza

May 22, 2018

Cikin kwanakin da suka gabata artabu tsakanin dakarun Isra'ila da Falasdinawa masu zanga-zanga da ke killace a Zirin Gaza ya nuna irin matsalolin da rashin makoma da mazauna yaniin ke ciki.

https://p.dw.com/p/2y6Pp
Drohnen und Drachen überfliegen Gaza-Proteste
Hoto: Reuters/I.A. Mustafa

Fiye mutane 100 yayin da wasu 10,000 suka jikata lokacin artabu da jami'an tsaro. Dama tuni rayuwa ta tabarbare a Zirin Gaza, inda Majalisar Dinkin Duniya ta cewa nan da shekara ta 2020 rayuwa za ta gagara a Gaza cikin wani rahoton watan Yuli na shekarar da ta gabata ta 2017.

Marc Frings na gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus a Ramallah ya ce tuni aka kai ga wannan matsaya saboda matsalolin karancin ruwa da makamashi sun kai mizani mafi sukurkucewa da ya kai ga samun cutar amai da gudawa da wasu matsalolin masu nasaba da lafiya.

Drohnen und Drachen überfliegen Gaza-Proteste
Hoto: Reuters/A. Cohen

A farkon shekara ta 2000 kashi 98 cikin 100 na mutanen Gaza suna tsaftaceccen ruwan sha, amma zuwa shekara ta 2014 adadin ya koma kashi 14 cikin 100. Wasu matsalolin suna da danganta da kungiyar Palasdinawa ta Hamas da cin hanci ya yi katutu. Sannan da toshen yankin da Isra'ila ta yi, Omar Shakir ya kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ya nunar.

Palästina Israel Gaza Protetste Verletzte
Hoto: Getty Images/AFP/S. Khatib

Omar Shakir ya kara da cewa rashin aiki ya kai kashi 50 cikin 100 tsakanin matasa na Gaza, inda tsakanin mata rashin aikin ya kai kusan kashi 80 cikin 100. A daya bangaren Jamie McGoldrick babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kasashen Gabas ta Tsakiya ya ce yanayin da ake ciki ya nuna babu sauran fata ga mutanen Gaza.

Sannan Jamie McGoldrick ya ce yanayin ya janyo karin matasa masu kashe kansu saboda kuncin rayuwa da matsaloli na kwakwalwa.