Gasar wasan dambe
May 2, 2017Talla
Wannan gagarumin ƙwazo ya sa Joshua mai shekaru 27 da haihuwa ci gaba da rike kambunsa ta IBF. Sannan kuma ya kwace lambar zakaran boksin ajin masu nauyi ta duniya daga hannun Wladimir Klitschko mai shekaru 41 a filin wasa na Wembley.
'Yan kallo kimanin dubu 90 ne suka shaida karawar da aka shafe zagaye 11 ana yinta kafin Anthony Joshua ya kai abokin karawarsa kasa bayan wani wawan naushi da ya sa alkali tsayar da wasa.
Shi dai Anthony Joshua, wanda iyayensa 'yan Najeriya ne, ya taba lashe lambar zinariya ta dubiya a wasannin Olympik na 2001. Sannan kuma wannan shi ne karo na 19 da ya nuna bajintar lashe damben da fintikau.