1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar neman cin kofin duniya ta mata

Mouhamadou Awal Balarabe
August 17, 2023

Gasar kwallon kafa ta neman cin kofin duniya ta mata na zama ta tara da FIFA ta shirya, wanda ya hada kungiyoyin mata 32. A wannan karon ta faru a Ostiraliya da New Zealand daga 20 ga Yuli 20 zuwa 20 ga Agusta 2023.

https://p.dw.com/p/4VHuP
'Yan matan Ostareliya sun yi nasarar hayewa matakin karshe na kofin duniyaHoto: Steve Christo/AFP/Getty Images

A zagayen farko na gasar, an fitar da 'yan matan Jamus da suka taba rike kofin duniya sau biyu (2003 da 2007) da kuma 'yan matan Kanada da ke rike da kofin gasar Olympics, yayin da Sweden ta fitar da Amurka da ta lashe gasar sau biyu ta fita a zagaye na gaba. Wasan karshe da ba a taba yin irinsa ba zai gudana ne tsakanin Ingila da Spain, wadanda suka fitar da Ostareliya da Sweden a wasan kusa da na karshe. Su ma wakilan Afirka ciki har da Najeriya da Maroko duk an yi wajen road da su.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna