Gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Jamus | Labarai | DW | 09.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Jamus

A yau ake fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a nan Jamus, inda za´a yi karawar farko tsakanin Jamus mai masaukin baki da kuma kasar Costa Rica a birnin Munich dake cikin jihar Bavaria. Da karfe 6 agogon Jamus wato nan da kusan sa´o´i 3 masu zuwa za´a kaddamar da wasan, bayan an kammala shagulgulan bude gasar cin kofin na duniya wanda shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler zai jagoranta. Mai koyar da ´yan wasan Jamus Jürgen Klinsmann ya ce ´yan wasan sa ba zasu raina ´yan wasan Costa Rica ba, domin kamar yadda masu iya magana kan ce ne wai dan hakin da ka raina shi ke tsone ma ido. A birnin Berlin SGJ Angela Merkel ta karbi bakoncin shugaban Costa Rica Oscar Arias Sanchez. Dukkan shugabannin biyu dai zasu kalli karawar a birnin Munich. A jawabinsa shugaba Sanchez ya ce yayi imani mabugan kwallon kafar dake wakiltar kasar sa a gasar cin kofin kwallon kafar na duniya zasu yi rawar gani.