1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FIFA: Maroko ta kafa tarihi a Katar

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 15, 2022

A daidai lokacin da ake shirin kammala gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ke gudana a yanzu haka a kasar Katar, ana ci gaba da jinjina ga 'yan wasan kasar Maroko da suka wakilici Afirka da ma kasashen Larabawa.

https://p.dw.com/p/4L1VK
FIFA  2022 | Wasa | Faransa | Maroko | Achraf Hakimi | Kylian Mbappé
Afirka ta kafa tarihi a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ta KatarHoto: Christophe Ena/AP Photo/picture alliance

Marokon dai ta kasance kasar Afirka tilo da ta taba kai wa wasan kusa da na karshe, tun bayan fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da hukumar FIFA ke shiryawa. Koda yake Maroko ta gaza kai bantenta, ana ci gaba da jinjina ga 'yan wasanta da ma fatan dorewar wannan nasara da aka bayyana da ta nahiyar Afirka baki daya har ma da kasashen Larabawa.

A wasan kusa da na karshen da suka fafata da Faransa, Marokon ta mamaye wasan musamman bayan an dawo hutun rabin lokaci. Sai dai duk da irin kwazon da 'yan wasan na Atlas Lions suka nuna Faransan ta lallasa su da ci biyu da nema, lamarin da ya sanya suka gaza kai wa ga wasan karshe da zai daukaka tarihin nahiyar Afirkan da suka kafa.