1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gasar cin kofin ƙwallo ta duniya

Aski ya zo gaban goshi a gasar cin kofin ƙwallo ta duniya, inda Jamus ke karawa da Yurugai

default

Jamus za ta kata da Yurugai a filin wasan Port Elizabeth

A cigaba da gasar cin kofin ƙwallo ta duniya da ake gwabzawa a ƙasar Afrika ta Kudu, a wannan Asabar ake fafatawa tsakanin Jamus da Yurugai domin tantance ƙasar da za ta maye gurbi na ukku. Tashar rediyon DW za ta watsawa kai tsaye wannan wasa da zai wakana a filin ƙwallon Port Elizabeth.

A yayin da ya ke bayyani akai shaharraren ɗan wasan nan na Jamus Thomas Müller cewa yayi:

"Ina kyautata zaton a wannan karo Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Jamus za ta buga wasa na ƙwarai. Hakan ya zama wajibi gare mu ta yadda za mu kammala wasan cikin nasara".

Gobe idan Allah ya kai mu, Spain za ta buga wasan ƙarshen da Holland.

A cen ƙasar ta Holland, gwamnatin ta ɗauki dokar hana shan barasa a wuraren da aka keɓewa jama´a domin kallan gasar. Gwamnatin ta yi hakan da zumar yin rigakafi ga abkuwar haɗarrurruka.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohamed Nasiru Awal