1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fitar da rukunan ƙasashen da za su kara a gasar ƙwallon kafa ta 2010

Sadissou YahouzaDecember 5, 2009

Hukumar FIFA ta bayyana rukunan ƙasashen da zasu kara a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya a Afrika ta Kudu daga 11 ga watan Juni zuwa 11 ga watan Juli shekara ta 2010

https://p.dw.com/p/KqzI
Joseph Blatter Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFAHoto: AP

Bayan da Hukumar wasan ƙwallon ƙafa ta duniya wato FIFA ta fitar da sunyayen ƙasashen da zasu fafata a zagayen farko na wasan cin kofin duniya da za'a fara a ƙasar Afirka ta Kudu. Masu sha'awar wasan ƙwallon ƙafa na ciki da wajen nahiyar suna ci gaba da yin sharhi game da rukunan da ƙungiyoyin wasan ƙwallon ƙafa guda shida dake wakiltar nahiyar suka samu kansu a ciki.

Sakamakon da aka fitar a ranar juma'a nan dai ya nuna cewar mai masaukin baƙi wato Afirka ta Kudu tana rukunin A ne, inda kuma zata buɗe wasa da ƙasar Mexiko, sai kuma Uruguay da Faransa. A yayinda Najeriya ke rukunin B tare da Argentina da Koriya ta Kudu da kuma Girka. ƙasar Algeriya kuwa tana rukunin C ne tare da Ingila da Amurka da Sloveniya.

Sauran ƙasashen Afirka da suka samu kaiwa ga wannan wasa dai,wato Ghana na rukunin D ne tare da Australiya da Sabiya da Jamus. A yayin da Kamaru ke rukunin E tare da Holland da Denmark da Japan. Ita kuwa Ivory Coast tana rukunin G ne tare da Brazil da Koriya ta Arewa da Portugal.

Italiya kuwa na rukunin F ne tare da Paraguay da New Zealand da Slovakiya, sai Spain dake rukuni ɗaya da Switzerland da Honduras da Chili.

Tuni dai masu sharhin wasan kwallon ƙafa na ciki da nahiyar Afirkan suka fara tofa albarakacin bakunansu game da rukunan da ƙasashen Afirka suka samu kansu a ciki.

A yayin da wasu suka baiyana rukunin D da ya ƙunshi ƙasashen Ghana da Jamus da Australiya da Sabiya a matsayin mafi zafi. Babban kocin 'yan wasan Jamus Joachim Löew ya bayana fatan a tashin farko Jamus zata samu nasara akan ƙasar Australiya, domin kuwa ƙasar Ghana data kasance ƙasar farko data cancanci shiga wasan bayan Afirka ta kudu mai masaukin baƙi ba kanwar lasa bace, musanman idan aka duba tarihin wasannin da suka buga a baya.

WM2010 Südafrika Auslosung Gruppenphase Englisch A-D
Rukunin ƙungiyoyi A-D a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya

Loew yace Ghana itace ƙasa mafi ƙarfi ta harkar wasanni a nahiyar ta Afirka yanzu, koda yake akwai Ivory Coast. Amma nasan tana da 'yan wasa dake wasa anan Jamus. Kaga akwai Micahel Essien dake wasa da Michel Ballack a ƙungiya ɗaya na ƙoƙoluwan wasan ƙwallo.

Rukunin G daya ƙunshi Brazil data taɓa cin kofin duniyan har sau biyar da Portugal da kuma Ivory Coast da akewa kallon ɗaya daga cikin zakarun Afirka da Koriya ta Arewa dake zama sabon shiga a gasar cin kofin ta duniya, anan ma ana ganin ƙasar Ivory Coast zata baiwa maraɗa kunya,musanman idan akayi la'akari da 'yan wasa irin su Drogber da shima ke wasa a Turai.

WM2010 Südafrika Auslosung Gruppenphase Englisch E-H
Rukunin ƙungiyoyi E-H a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya

Sauran ƙasashen Afirka a wannan gasa dai sun haɗa da Aljeriya dake rukuni ɗaya da Amirka da Ingila da Sloveniya, kuma koda yake Algeriyan ba kanwar lasa bace wajen taka ledan a nahiyar,amma kuma haɗuwa da ƙasashe irin su Ingila da kuma Amirka da yanzu haka take neman suna a wasan da ada bata ɗauke shi da mahimmanci ba, ana ganin sai ta tashi tsaye.

Suma 'yan Najeriya hamdala suka nuna a yayin da Super Eagles ta sauka a rukuni ɗaya da Arjentina da Koriya ta Kudu da Girka.

Nigeria Nationalmannschaft FiFA 2010 Weltmeisterschaft Südafrika Flash-Galerie
'Yan ƙungiyar Super Eagles na NajeriyaHoto: dpa

Yanzu dai a yayin da ya rage watannin shida a fara wannan gasar kuma masu sharhi keci gaba da bayyana ra'ayoyin su don gane da rukunan da ƙasashen su suka samu kansu a ciki. Shahararren ɗan wasan duniya kuma Kocin Argentina wato Diego Maraddona, wanda yanzu hukumar FIFA ta dakatar dashi, yace duk wata ƙungiya data samu nasarar kaiwa ga gasar ƙarshe na cin kofin Duniya...ba abun rainawa bace, kuma ba'a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare a wannan gasa dake da mahimmancin gaske ga ƙasashen nahiyar Afirkan.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi