Garkuwa da 'yan majalisa a Banizuwela
July 6, 2017A Banizuwela 'yan majalisar dokokin bakwai da wasu ma'aikatan majalisar kasar kimanin 10 ne suka ji rauni a lokacin da wasu daruruwan magoya bayan Shugaba Nicolas Maduro dauke da kulake da wukake da kuma duwarwatsu suka kutsa da karfi a cikin ginin majalisar wacce 'yan adawa ke da rinjaye a cikinta tare da yin garkuwa da 'yan majalisar da ma 'yan jarida a tsawon awoyi tara.
Sai a cikin daren jiya ne jami'an 'yan sanda dauke da kayansu na sulke sun kutsa a cikin majalisar inda suka yi nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su daga hannun masu zanga-zangar. Sai dai kuma Shugaba Nicolas Maduro ya nisanta kansa da mutanen da suka yi garkuwa da 'yan majalisar yana mai cewa ba shi da hannu ko miskala zarratun a cikin lamarin tare ma da yin Allah wadai da shi.
Watanni da dama kenan da masu adawa da milkin shugaba Nicolas Maduro ke gudanar da zanga-zangar neman tilasta masa yin murabus daga kan mukaminsa na shugabancin kasar a bisa zarginsa da yi wa kundin tsarin mulkin kasar karan tsaye da kuma kasa shawo kan matsalolin tattalin arzikin da kasar ke fama da su a shekarun baya bayan nan.