Garkuwa da maáiktan mai a yankin Niger Delta | Labarai | DW | 07.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garkuwa da maáiktan mai a yankin Niger Delta

Yan takife a Nigeria sun kai farmaki a kan wasu rijiyoyin mai a kudancin ƙasar inda suka kashe a ƙalla sojoji biyar tare kuma da yin garkuwa da wasu yan kwangila biyar yan ƙasar Koriya ta kudu. ƙungiyar yan takifen tace farmakin da suka kai cibiyoyin man na kamfanin Shell mataki ne na maida martani a game da hukuncin da kotu na ƙin bayar da belin shugaban ta Mujahid Dokubo Asari wanda ke fuskantar sharia kan laifin cin amanar ƙasa. ƙungiyar ta ƙara da cewa yan Koriya ta kudun da tayi garkuwa dasu, suna cikin ƙoshin lafiya kuma ba za ta illata su ba, har sai in an kai musu hari ne a sansanin su. Kwanaki uku da suka wuce aka sako wasu turawa takwas maáikatan mai da wata ƙungiyar yan takifen ta yi garkuwa da su.