Garanbawul a rundunar sojin Nigeria | Labarai | DW | 30.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garanbawul a rundunar sojin Nigeria

Shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo ya gudanar da garanbawul na wasu manyan kwamandojin sojin ƙasar a wani abu dake zama ba zata gabanin zaɓe da ƙasar ke shirin gudanarwa a shekara mai zuwa. Sanarwar data fito daga fadar shugaban ƙasar ba ta bada wasu dalilai na yin garanbawul ɗin ba. A ƙarƙashin sauyin Obasanjon ya maye gurbin uku daga cikin manyan kwamandojin sojin huɗu wanda ya haɗa da mai bashi shawara kan alámuran tsaron ƙasa Alhaji Aliyu Gusau inda aka maye gurbin sa da Sarki Mukhtar. Sai janar Martin Luther Agwai wanda aka ɗaga likafar sa zuwa babban hafsan hafsoshi na ƙasar. Tuni dai dama ake ta raɗe raɗi a game da saukar Aliyu Gusau cewa yana so ya tsaya takarar neman shugabancin Nigeria. Sauyin dai ya zo ne makwanni biyu kacal bayan da majalisun dokokin ƙasar suka yi wasti da batun tazarce wanda zai baiwa Obasanjo damar cigaba da mulki a karo na uku.