Garanbawul a majalisar Ministocin Nigeria | Labarai | DW | 21.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garanbawul a majalisar Ministocin Nigeria

Shugaban Nigeria Olusegun Obsanjo ya yi garanbawul a majalisar zartarwar kasar tare da sauyawa wasu ministoci guraben ayyuka. A karkashin garanbawul din Ministan kudi Ngozi Okonjo Iweala a yanzu zata kasance minista mai kula harkokin kasashen ketare, yayin da mataimakiyar ta Esther Nenadi Usman ta maye gurbi a matsayin minitan kudi. Tsohon ministan harkokin wajen Olu Adeniji a yanzu an maida shi maáikatar alámuran cikin gida.. Haka kuma shugaba Obasanjon ya kuma rantsar da sabbin ministoci wadanda suka hada da na Ilimi da alámuran wassani dana aládu da yawon bude idanu da kuma ministan albarkatun ruwa.