1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garambawul ga manufofin jin dadin rayuwar jama'a a Jamus a shekara ta 2003

December 24, 2003
https://p.dw.com/p/Bvmv
Kawo yanzun dai babu wata gwamnati da aka yi a nan kasar ta Jamus wacce tayi kurarin gabatar da wasu tsauraran matakai na samar da ga manufofin jin dadin rayuwar jama'a tun daga tushensu, sai dai wasu 'yan kwarya-kwaryar matakai, wadanda ke taimakawa wajen lafar da radadin matsalolin da ake fama da su amma ba warkar da wadannan matsaloli kwata-kwata ba. Amma fa a daya hannun kasar tayi shekaru gwammai tana samun sauye-sauyen matsayin yawan al'umarta. A sakamakon haka gwamnatin hadin guiwa ta SPD da the Greens, akalla a wa'adin mulkinta karo na biyu, ta ga ba makawa face ta gabatar da matakan canji domin tinkarar wannan kalubala ta bunkasar tsofaffi da yawan marasa aikin yi. Jim kadan bayan nasarar zaben da aka gudanar shekarar da ta wuce, shugaban gwamnati Gerhard schröder ya ba da sanarwa a game da tsauraran matakai na garambawul da gwamnatinsa zata dauka. Tun kuwa tafiya bata je nesa ba gwamnatinsa ta fara fuskantar tofin Allah tsine daga al'umar kasa da sauran kungiyoyi. Sama da mutane dubu dari daga sassan Jamus dabam-dabam suka shiga zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin a cikin watan nuwamba. Wannan zanga-zanga ita ce mafi tsanani da gwamnatin Schröder ta shaidar tun bayan gabatar da kundin da aka kira wai "Agenda 210", wanda ya kunshi tsauraran matakai na garambawul ga kasuwar kodago da manufofin kyautata jin dadin rayuwar jama'a. A lokacin da yake bayani game da haka shugaban gwamnati Gerhard Schröder cewa yayi: "Wir müssen die sozialen Sicherungssysteme neu justieren, nicht um.... Wajibi ne mu aiwatar da gyare-gyare ga tsare-tsaren jin dadin rayuwar jama'a domin ta haka ne kawai za mu iya kare makomar wadannan manufofi, a maimakon mu kayyade su ko kuma mu kawar da su baki daya. Wannan matakin zai shafi kowa-da-kowa, ba kawai sai wani bangare na al'umar kasa ba. ....Opfer von vielen, keineswegs nur von einer Bevölkerungsgruppe." To sai dai kuma a yayinda al'umar kasa, sannu a hankali, suka fara hakikancewa da gaskiyar wannan batu, sauran kungiyoyi sun tashi tsaye domin hana wanzuwar matakan na gwamnati. Sai da ministar kula da zamantakewar jama'a Ulla Schmidt ta tashi tsaye wajen wayar da kan likitoci da kyamis da sauran jam'an kiwon lafiya da cewar matakan garambawul a manufofin kiwon lafiya sun shafi kowa-da-kowa ne ba su kadai ba. "Unsere Gesunheitspolitik hat ein klares..... Manufofinmu na kiwon lafiya suna kan wata tsayayyar turba ce ta kara aminta kiwon lafiya da riga kafi ga kowa da kowa, ba nuna gata ga wani bangare na al'umar kasa ba, kamar yadda wasu masu neman hana ruwa gudu ke ikirari. Kuma a saboda haka zamu ci gaba akan wadannan matakai na garambawul ta yadda dukkan mutane zasu ci gajiyar nagartattun hanyoyin kiwon lafiya a nan kasar. ....dass gute Gesunheitsvorsorge für alle bezahlbar bleibt." A hakika dai duk da sabanin da ake ci gaba da fuskanta a game da daidaituwar da aka cimma tsakanin gwamnati da ‚yan hamayya akan matakan na garambawul, wadanda ake ganin cewaer majiyyata ne zasu fi jin radadinsu, amma fa tilas ne a aiwatar da canje-canje ba ma kawai ga manufofin kiwon lafiya ba har da sauran manufofin da suka shafi makomar jin dadin rayuwar jama'a a nan Jamus. Babban abin da ya fi ci wa jama'a tuwo a kwarya dai shi ne maganar garambawul ga tsarin fansho. Shekaru biyu bayan shawarar garambawul ga manufofin fansho da tsofon ministan kodago Walter Riester ya gabatar, gwamnati ta sake tsayar da wata sabuwar shawara ta yin gyara. Bisa ga ra'ayin gwamnatin ta hadin guiwa tsakanin SPD da the Greens wajibi ne a samu canji ga matsayin fanshon da ya hada da yawan kudaden fansho da kuma yawan shekarun fansho. A karkashin matakan gyarar fuska da gwamnati ta dauka akan shawarar ta Riester za a rage yawan kudaden fanshon daga kashi 48% na jumullar abin da ma'aikaci ya saba samu a shekara zuwa kashi 40% na da shekara ta 2030. A baya ga haka gwamnati na neman dakatar da manufar nan ta fansho na gaba da wa''di, wacce da yawa daga kamfanoni suka rika amfani da ita domin maye gurbin tsaffin ma'aikatansu da matasa masu ji da jini a jika. Wannan manufa kuwa tana mummunar tasiri akan baitul-malin gwamnati. A hakika dai gaba daya marasa aikin yi su ne zasu fi jin radadin matakan garambawul din na gwamnati, inda za a rage yawan watannin taimakonsu daga watanni 32 zuwa 18. A takaice dai dukkan wadannan matakai, kamar yadda ake yayatawa, somin tabi ne, akwai wasu tsaurara da zasu biyu baya nan gaba. To masu sauraro da wannan muke kammala shirin MKT na wannan rana sai kuma mako mai zuwa idan Allah Ya kaimu. A madadin abokan aikina Zainab Ahmad Muhammed da Yahouza Salisu Madobi da suka taya ni gabatar da shirin ni ATL nake cewar a huta lafiya daga nan birnin Cologne.