Garambawul a rundunar Amirka dake Afganistan | Siyasa | DW | 12.05.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Garambawul a rundunar Amirka dake Afganistan

A wani mataki na ba zata Amirka ta sauke Janar David Mckiernan,babban Kommadan sojojinta dake ƙasar Afganistan

default

An tsige Janar David Mckiernan daga shugabacin rundunar Amirka a Afganistan

A wani mataki na ba zata, Amirka ta sauke Janar Mckiernan, daga matsayin babban kommandan sojojinta a ƙasar Afganistan.

Sakataran tsaron Amirka Robert Gates ya bayyana labarin cenjin da sunan shugaban ƙasa Barack Obama.

Bayan shekara ɗaya kacal da yayi ya na jagorancin rundunar sojojin Amuruka a Afganista Janar David Mckiernan zai sauka.

Za a maye gurbinsa da Janar Stanley McChristal daya daga kurraru soja na kasa.

Wannan cenji ya wakana kwanaki kaɗan bayan da shugaba Barack Obama ya lunka yawan sojojin a Afganistan zuwa dubu 68.

sakataran tsaron Robert ya bayana dalilan da suka kai a ɗaukar matakin cenza Janar David Mckiernan:A yanzu mun ƙaddamar da wata sabuwar siyasa a Afganistan tare da sabin dubaru wanda shugaban ƙasarmu ya ɓullo da su.

Kazalika muna da sabuwar taswira, saboda idan kiɗi ya cenza wajibi ne rawar ma ta cenza.

Janar David Mckiernan ya fara jagorancin sojojin Amirka a Afganistan a watan Juni na shekara da ta gabata.

Bayan hawan shugaban Obama karagar mulkin Amirka ya ɓullo da wani sallo, wanda aiyanar da shi ya fi dacewa da saban shugaban kommandan sojojin da aka naɗa , domin cemma a shekara ta 2001 ya taɓa jagorantar wata runduna ta mussamman da Amirka ta aika a Afganistan,inda ya samu babbar nasara, haka zalika a Irak.

A cewar Sakataran tsaron Amrika Robert Gates babu kwankwanto, janar Stanley McChristal zai taka rawar gani bisa cimma burin da aka sa gaba a ƙasar Afganistan:
Idan akayi la´akari da sabuwar husa´a, a sabuwar taswira da kuma saban yanayi da hukumomin ƙasar da kuma ƙasashe duniya suka ƙaddamar a Afganistan, lokaci ne na daidai da yin cenji.

Babban yaunin da ya rataya kan saban kommandan sojojin Amirka a Afganistan shine maido doka da ioda a faɗin ƙasar baki ɗaya ta hanyar murƙushe ´yan Taliban.

Saidai akwai buƙatar wannan aiki ya gudana tare kiyaye rayukan fara hula.

A ɗaya hannun sakataran tsaran Amurika , yayi yabo da jinjina dantse ga kommandan mai barin gado, wanda shima inji Gates ya gudanar da kyakyawan aiki.

A yanzu ayar tambaya itace ta ƙaƙa saban jagoranci zai ɓullo ma ´yan Taliban idan akai la´akari da yadda suke gasawa sojojin Ƙungiyar tsaro ta NATO aya a hannu ?

Tun shekara ta 2001 Amurika tare da haɗin gwiwar sojojin taron dangi,suka kifar da mulkinTaliban a ƙasar Afganistan suka kuma ƙaddamar da wani gagarami shiri a ƙarkashin Ƙungiyar tsaro ta NATO, domin gamawa kwata-kwata da Ƙungiyar , to saidai a wani mataki na ana magani kai na kaɓa sojojin ƙasa da ƙasa na fuskantar turjiya mai tsanani daga mayaƙan Taliban.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi.

Edita: Mohamed Nasiru Awal