1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gano daya daga cikin 'yan matan Chibok

Ana kara samun bayanai bayan gano daya daga cikin 'yan matan Chibok a Jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Ana kara samun bayanai kan gano daya daga cikin 'yan mata 'yan makaranta na Chibok wadanda tsagerun kungiyar Boko Haram suka sace fiye da shekaru biyu da suka gabata. Iyayen da shugabannin al'uma sun tabbatar da labarin cewa jami'an tsaro sun gano wannan yarinya. Jami'an tsaron sa-kai na JTF suka gano Amina Ali cikin daren Talata.

Fiye da shekaru biyu da suka gabata aka sace 'yan mata 'yan makaranta 219 da aka sace daga garin Chibok na Jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ke hannun tsagerun Boko Haram, bayan wasu daga cikin daliban sun kubce tun ranar da aka yi garkuwa da su. Gwamnatin Najeriya karkashin Muhammadu Buhari da ta dauki madafun iko cikin shekarar da ta gabata ta yi alkawarin kawo karshen rikicin tsagerun na Boko Haram da ya kai ga mutuwar dubban mutane.

Sauti da bidiyo akan labarin