Gangamin yan adawa a Kampala,Uganda | Labarai | DW | 06.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gangamin yan adawa a Kampala,Uganda

Jamian yansanda sunyi ta harba barkonon tsohuwa wa taron gangami na yan adawa adandalin taron kamfala,duk da haramta taron da jamian yansanda sukayi.Shugabar rundunar yansanda na birnin Kafala Grace Turyagumanawe,ta fadawa manema labaru cewa sun cafke wasu membobin jammiyar adawa ta Democrat ,sakamakon tsayin daka da sukayi kann gudanar da wannan gangami nasu.Ta shaidar dacewa,an umurcesu dasu dage gudanar da taron a wannan cibiya,domin gudun kada su kawo tsaiko cikin harkokin kasuwanci da gufdanarwa,amma sukayi watsi da umurnin.An dai dakatar da shugaban jammiyar adawar Ssebaana Kizito da sauran jamian sa daga isa cibiyar gangamin,inda akesaran suke shirin gabatar da wani rahotan bincike dangane da kisan gilla da akayiwa tsohon minista a gwamnatin shugaba Yoweri Museveni,shekaru 20 da suka gabata.