1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasa sun kaddamar da yaki da fyade

March 1, 2017

Matasa a Jihar Katsina da ke Najeriya sun kaddamar da shirin yaki da fyade da wayar da kai.

https://p.dw.com/p/2YS3e
Symbolbild - Verschleierte Frau in Nigeria
Hoto: Getty Images

A Jihar Katsina ta Najeriya wasu matasa sun kafa wata kungiya suna gangamin fadakar da Al,umma game da lafiyar mata da kananan yara musamman abunda ya shafi fyade. Wadannan matasa dai suna yin wannan gangamin fadakarwa ta hanyar kafafen yada labaruai gami da yin turuka ta la'akari da yawaitar fyade wanda kuma iyaye na boye irin wannan aika-aika.

A irin fadakarwar wadannan matasa sukan ja hankalin iyaye da ganin sunkai rahotan duk wanda aka samu yayiwa wata yarinya fyade gaban mahukunta dan hukunci da doka ta tanadar a cewar shugaban kungiyar Abdullahi Aliyu katsina.

Shugaban kungiyar ya kara da cewa duk wata shaida wadda zata tabbatar idan an samu wanda aka kama da wannan aika aika to a gabatar da ita ga mahukunta.

A wani babban taro da wannan kungiya ta shirya wanda ya tattara mata daga kananan hukumomi 34 da ke fadin jihar ta Katsina inda aka gabatar da kasidu kala-kala game da dakile matsalar fyade a jihar Amina Lawal Dauda ita ce jami'ar da ke kula da gamayyar kungiyoyin matan jihar katsina ta jinjinawa kokarin wannan kungiya a wurin taron.

Sha'anin fyade dai abu ne da ya zama ruwan dare duk kuwa da matakan da hukumomi suka ce suna dauka sai dai ba sa samun cin nasarar dakile wannan iftila'iba ba tare da da hadin kan iyaye ba.