1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin tunawa da Hariri

February 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuRl

Kimanin alummominin laebanon dubu 300 ne suka gudanar da wani gangami yau abirnin Beirut ,domin tunawa da marigayi tshohon prime minista Rafik al hariri wanda akayi wa kisan gilla shekaru biyu da suka gabata.,tare da bayyana goyon bayansu wa gwamnatin kasar da Syria ke adawa da ita.Jamian yansanda dai sun kewaye makabartar tsohon prime ministan dake dake tsakiyar cibiyar binne wadanda suka salwantar da rayukansu wa kasar,inda aka rubuta lamba 730,wanda ke nufin kwanaki 730 ba tare da an gurfanar da wadanda keda alhakin kisan gaban kotu ba.Andai cigaba da gudanar da wannan gangamin ayau,ba tare da laakari da boma bomai sda suka tarwatse guda biyu jiya a birnin Beiruta ba.Harin da gwamnatin Lebanon din ta zargi Syria da aikatawa,harin daya kashe mutane 3 ,tare da raunana wasu guda 20.