1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana gangamin karsahe na yakin neman zaben Turkiyya

Suleiman Babayo
June 22, 2018

'Yan takara shida za su fafata a zaben na Turkiyya da ake sa ran Shugaba Recep Tayyip Erdogan sai samu sabon wa'adi na mulki.

https://p.dw.com/p/3073Z
Türkei Kundgebung zur Unterstützung von Erdogan in Istanbul
Hoto: Reuters/O. Orsal

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya yana gangamin karshe na yakin neman zaben shugaban kasa a birnin Santambul. Akwai 'yan takara guda shida da ke fafata zaben ranar Lahadi.

Kuma Shugaba Erdogan ake ganin zai samu nasara yayin wannan zabe da ke tafe. A shekara ta 2017 aka gyaga ga kundin tsarin mulkin kasar ta Turkiyyya inda aka kara karfin shugaban kasa maimakon firaminista. Daukacin 'yan takara suna yunkurin karshe na jan ra'ayin masu kada kuri'a.