Gangamin goyon bayan Mugabe a Zimbabuwe | Siyasa | DW | 25.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gangamin goyon bayan Mugabe a Zimbabuwe

An dai sami mabanbantan ra'ayoyi kan gangamin goyon bayan shugaban tsakanin matasan kasar inda wasu ke masa kallo na dan kama karya, da ke zama dan mutu ka raba da kujerar mulki.

Simbabwe Proteste in Harare

Matasa da suka halarci gangamin goyon bayan Mugabe

Gangamin na matasan kasar miliyan daya sun shirya shi ne domin nuna goyan baya ga shugabancin Robert Mugabe wanda ya shafe shekaru 36 na mulki a kasar ta Zimbabuwe. A kalla dai matasa dubu dari ne wadanda suka fito daga cikin lardina goma na kasar ake saran su halarci bikin gangamin a inda aka shirya cewar shugaba Mugabe zai gabatar da jawabi ga dandazon taron matasan.

Da kadan da kadan dai farin jinin shugaba Robert Mugabe na ci gaba da ja da baya sakamakon karuwar tabarbarewar tattalin arziki gami da tarin matsaloli a harkokin yau da kullum.

Wasu daga cikin matasan Zimbabuwe sun tofa albarkacin bakinsu a yayin da suka tattauna da tashar DW kan yadda suke kallon gangamin nuna goyan bayan ga Mugabe:

Simbabwe Proteste gegen Mugabe

Akwai dai matasa da suka yi hannun riga da mulkin na Mugabe

"Ko tantama babu ga batun salon shugabancin Robert Mugabe, daukacin nahiyar Afirka da duniya baki daya sun san shi." a cewar wani matashi.

Sai dai ba duka matasan kasar ke goyon bayan shugaban ba kamar yadda wannan matashin shi kuma ya nunar:

"Matasan wannan karnin na cikin tsaka mai wuya kuma lokaci na tafiya, ba ma wani abu ba kuma ma samun ci gaba."

Duk da dai tarin matsin lambar da Mugaben ke samu, shugaban na kan karaga kuma na matukar bukatar ganin an sake zabarsa a shekara ta 2018 duk kuwa da cewar shekarunsa sama da 90 a duniya.

Masana dai na nuni da cewar gangamin na ranar Larabar nan na iya lakume Dala dubu 600 a yayin da mataimakin sakataren rundunar matasan ta jam'iyyar ZANU PF ke cewa masu sukar lamirin shugaban mafarki ne suke yi.

Simbabwe Präsident Robert Mugabe

Shugaba Mugabe

"Mun yi amannar cewar Shugaba Mugabe shi ne mutum daya tilo daya jagoranci 'yanto kasar daga hannun Turawan mulkin mallaka, babu abin da ya shalli matasa da shekarunsa ko da kuwa ya kai shekaru 125, muddin dai ya na tabukawa kuma na hangen nesa wajen ci gaban kasar, za mu ci gaba da zabarsa.

Gangamin wanda ya somo asali daga wani fasto matashi wanda ya yi wa lakabi da "Thisflag" mafi yawan matasan Zimbabuwe ke amfani da shi a kafafen sada zumunta wajen mayar da martani kan gwamnati.

Ko ma dai mene ne wala Allah a kafar dandalin sada zumuta ko akan titunan Harare farin jinin Robert Mugabe dai na ci gaba da zama babbar muhawara.

Sauti da bidiyo akan labarin