1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar tsakanin Egelan da shugaban LRA na Uganda

Hauwa Abubakar AjejeNovember 13, 2006

Babban jamiin kula da jin dadin jamaa na Majalisar dinkin duniya Jan Egeland ya gana da shugaban yan tawayen LRA na Uganda,sai dai kuma ya gagara samun nasasar sako mata da yara kanana daga cikin kungiyar.

https://p.dw.com/p/BtxS
Jan Egeland
Jan EgelandHoto: AP

Bayan an kwashe saoi da dama ana jiransa, shugaban yan tawayen LRA Joseph Kony,tare da matasa dauke da manyan makamai sun bullo daga kungurmin daji da suke boye a bakin iyaka Sudan da Jamhuriyar demokradiyar Kongo.

Sanye da korayen kaki da bakin madubi,Kony bai yi wasu maganganu da yawa ba a ganawar tasu da Egeland na mintuna 10.

Shi dai jakadan na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a sako mata da yara dake cikin kungiyar,amma Kony ya karyata cewa da yara cikin dakarun nasa.

Yace babu yara cikinmu,mayaka kadai muke da su kuma babu wani mai rauni cikinsu.

Egeland dai shine babban jamiin na kasa da kasa da ya taba ganawa da Kony.

Cikin shekaru 20 na yakin basasa,kungiyar LRA ta sace dubun dubatar mata da yara,domin kuwa yara da suka samu damar tserewa daga kungiyar, sun bada labarin irin tilasta masu da akeyi suna dukan yan uwansu har lahira ko kuma tilasta masu cin kwakwalwar wasu yaran.

Yanzu haka dai gwamnatin kudancin Sudan ce take shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya na Juba,hakazalika a yankin Ri-Kwangba inda yan tawayen suke ana basu abinci ruwa da matsuguni a kokarin dakatar da su daga yin fashi da kwasar ganima a kudancin Sudan da arewacin Uganda.

Tattaunawar zaman lafiyar ta ci tura bayan wani fada tsakanin bangarorin biyu a watan daya gabata.

Kony da mataimakinsa Vincent Otti,sunyi korafin cewa babban bainda ya hana ruwa gudu ga tattaunawar shine warantin tsare membobinsu 5 ne,ciki har da su kansu, da kotun kasa da kasa ta bayar.

Otti yace muddin dai aka janye batun tsare sun,to zasu koma teburin tattaunawa,wadda aka shirya da nufin kawo karshen daya daga cikin yakin basasa mafi muni a tarihin Afrika,wadda yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da tilasatwa fiye da miliyan 2 tserewa daga gidajensu.

Egeland dai yace LRA zata bada rahoto a ranar 22 ga wannan wata na ko akwai yara da mata ko wadanda suka samu ranui a wasu yankunan.

A cewarsa wannan ganawa tana da muhimmanci kwarai da gasket yace:

“ina ganin taro ne mai mahimmanci saboda a karo na farko na zauna da dukkan manyan shugabannin LRA ciki har da Joseph Kony na kuma baiyana masu yadda wannan yaki ya sanya jamaar arewacin Uganda cikin wahala,da muhimmancin ci gaba da tsagaita wuta da aka fara tun watan agusta,wannan itace fata mafi inganci cikin shekaru 20 na kawo karshen mummmunan yaki a arewacin Uganda”

To sai dai jamian LRA sunce da kyar ne Kony ya amince da bukatun Egeland na sako mata da yara,wanda daya daga cikinsu yace ba zasu su komawa gida ba.

Kafin ganawar tasu said a yan kungiyar ta LRA suka bincika motoci tare kuma da nuna adawa da kasancewar jamian tsaro na kudancin Sudan,wadanda daga bisani aka bar wasunsu a can nesa da inda akayi ganawar.