1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Trump da Buhari

Ramatu Garba Baba
April 30, 2018

Shugaba Donald Trump na Amirka zai gana da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a wannan Litinin, wannan shi ne karon farko da ya ke karbar bakuncin wani shugaba daga nahiyar Afirka bayan soma mulki.

https://p.dw.com/p/2wtIj
Kombobild Donald Trump und Muhammadu Buhari

Donald Trump ya gayyaci shugaba Muhammdu Buhari na Najeriya zuwa fadar White House, inda ake sa ran za su tattauna batutuwa da suka shafi yaki da ayyukan ta'addanci da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Trump ya sasha suka daga al'umma bayan da ya baiyana kasashen nahiyar Afirka a matsayin wulakantatu duk da cewa daga baya ya janye kalaman da ya ce rashin fahintarsa aka yi don kuwa ba hakan ya ke nufi ba.