Ganawar T.Blair da E.Olmert
September 5, 2007Talla
A cigaba da neman hanyoyin warware rikicin gabas ta tsakiya,wakilin mussamman na Majalisar Ɗinkin Dunia, ƙungiyar taraya turai, Amurika da Russia, wato Tony Blair ya gana yamacin jiya da Praministan Isra´ila Ehud Olmert.
Shugabanin 2, sun yi masanyar ra´ayoyi, a game da yiwuwar girka ƙasashe 2, wato Isra´ila da Palestinu, wanda za su maƙwabtaka irin ta cuɗe ni in cuɗe ka.
Sanarwar ƙarshen taro da su ka hiddo, ta bayyana sharuɗun da Isra´ila ta gindaya, kamin cimma wannan mataki.
Tony ya kyauttata zaton kai ga tudun dafawa a yunƙurin kawo ƙarshen rikici tsakanin Isra´ila da Palestinu, ta la´akari da haɗin kan da ya samu daga ɓangarorin 2.
To saidai a cewar sa,har yanzu, batun ƙungiyar Hamas, na ɗauke da babbar barazana.