Ganawar Strauss-Kahn da Ministan Girka a Washington | Siyasa | DW | 25.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ganawar Strauss-Kahn da Ministan Girka a Washington

Ana cigaba da yunkurin cimma yarjejeniya dangane da samar da ƙuɗaɗen ceton ƙasar Girka daga matsalolin tattalin arziki

default

Magabatan Girka da na Asusun bada lamuni na Majalisar Ɗunkin Duniya IMF sun sanar da cewar, ya zamanto wajibi a cimma yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu, kafin Girkan ta nemi tallafin biliyoyin Euro a matsayin kuɗaɗen ceto ta daga matsalolin tattalin arziki data faɗa.

Bayan ganawarsa da ministan harkokin kuɗi na Girka George Papacostantinou a birnin Washinton, shugaban asusun bada lamunin ta IMF Dominique Strauss-Kahn ya jaddada bukatar gaggauta cimma matsaya dangane da kuɗaɗen tallafin.

A cewar sa dai, bisa dukkan alamu nan bada jimawa ba ne za a cimma yarjejeniyar da zata kai ga bawa Girkan tallafin da take nema. Shi kuwa a ɓangarensa ministan kuɗin na Girka faɗawa taron manema labaru cewar, ganawar tasu mai armashi ce, duk kuwa da cewar ba zai iya cewa ga lokacin da ƙasarsa zata samu biyan bukatun nata ba.

Madrid Finanzministertreffen George Papaconstantinou

George Papaconstantinou

Gwamnatin Athens dai na bukatar kimanin dala biliyan 11 nan da 19 ga watan mayu, da karin biliyoyin daloli nan da ƙarshen shekara, idan har harkokinta zasu cigaba ta tafiya a wannan ƙasa.

A yanzu haka dai ana bin gwamnatin Girkan bashin dala biliyan 402, baya ga wasu sabbin kuɗaɗen da ake bukatar ta biya kafin ta samu sabon rancen.

Ƙungiyar Tarayyar Turai da hukumar bada lamunin ta IMF dai sun amince da bata dala biliyan 60, amma kashi biyu cikin ukun adadin zasu shiga asusun ƙungiyar ta EU.

Sai dai Jamus da ke kasancewa ƙasar da zata bada mafi yawan kuɗi wajen ceto Girkan, na iya ƙin amincewa da wannan yarjejeniya acewar ministan kuɗi Wolfgang Schaeuble. Ya ce kasancewar har yanzu ba'a cimma matsaya dangane da bawa Girkan wadannan kudaɗe, ta yiwu a bata ko kuma a fasa bata komai.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana mai ra'ayin yin taka tsantsan dangane da wannan yarjejeniya..

Merkel in Kalifornien

Angela Merkel

" Ta ce a ranar laraba mai zuwa zan gana da wakilan manyan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa anan fadar gwamnati. A wannan karon akwai wakilai daga Bankin Duniya, Hukumar IMF, OECD, ƙungiyar cinikayya ta Duniya da ta kwadago. Duk waɗannan ƙungiyoyin ƙasa da kasa ne da zasu bada gudummowa wajen tabbatar da ingancin rayuwa, kuma mun san da cewar muna bukatar dokoki na cimma hakan"

Za a bukaci Jamus da ke zama ƙasa mafi karfin tattalin arziki a ƙasashen 16 da ke amfani da kuɗin Euro dai akan ta bayar da gudummowar sama da dala biliyan 11, sai dai kowane agaji zata bawa Girkan na bukatar amincewar majalisar dokokin ƙasar.

A yanzu haka dai, hukumar gudanarwar Tarayyar Turan tayi nuni da cewar Jamus na da 'yancin hawa kujerar naƙi, wajen hana cimma yarjejeniyar bawa Girkan kuɗaɗen ceto ta daga durkushewar tattalin arzikin nata.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Mohammad Nasir Awal