Ganawar Solana da Jalili | Labarai | DW | 30.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar Solana da Jalili

Kantoman kula da harkokin waje na Ƙungiyar Taraiyar Turai Javier Solana,zai gana da babban mai shiga tsakani a batun nukiliya na Iran saoi kaɗan kafin ya mika rahotonsa ga Majalisar Ɗinkin Duniya kan batun nukiliya na Iran.Solana zai gana da Saeed Jalili cikin wata tattaunawa a London wadda ƙwarraru suka ce shine zai tabbatar da ko Amurka da ƙawayenta zasu ci gaba da bukatar sake laƙaba takunkumi kan Iran.Majalisar i ta bukaci Iran ta dakatar da inganta sinadaren uraniyum,Iran din a nata ɓangare tace shirinta na samarda hasken wutar lantarki ne ga jamaarta,amma duk da haka ƙasashen yammacin duniya sun haƙiƙance cewa tana shirin ƙera makaman nukiliya ne.