Ganawar shugabannin Rasha da Jamus da kuma Faransa | Labarai | DW | 19.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar shugabannin Rasha da Jamus da kuma Faransa

Shugaba Medvedev na Rasha ya tabbatarwa shugaba Sarkozy na Faransa da kuma Merkel ta Jamus cewar zai halarci taron koli na NATO

default

Shugaba Dmitry Medvedev na kasar Rasha ya sanar da cewar zai halarci babban taron kungiyar kawancen tsaron NATO da zai gudana a birnin Lisbon cikin watan gobe - idan Allah ya kaimu. A lokacin da ya ke yin jawabi a wajen taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Faransa da Rasha da kuma Jamus, shugaba Medvedev ya ce Rasha tana yin nazarin shirin da Amirka take yi na sanya na'urorin bada kariya ga makaman linzami a yankin gabashin Turai. A baya dai mahukunta a birnin Moscow na kasar Rasha suna daukar shirin sanya na'urorin a matsayin wata barazana ce ga sha'anin tsaron kasar su, amma Amirka ta ce hakan na da nufin bada kariya ce ga Turai daga hare haren da za ta iya fuskanta daga Iran ko kuma Koriya Ta Arewa.

Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wadda ta yiwa manema labarai jawabi bayan ganawar da suka yi da shugaban na Rasha da kuma shugaba Sarkozy na Faransa, bayyana jin dadin ta ne ta yi game da kudurin shugaba Medvedev na cewar zai halarci taron kungiyar kawancen tsaron NATO:

" Ina farin ciki matuka da shugaban Rasha Medvedev ya nunar da cewar zai halarci taron kolin kungiyar kawancen tsaron NATO a birnin Lisbon. Wannan wani albishir ne mai kyau, domin ya kamata a dora dangantaka tsakanin Rasha da NATO akan kyakkyawar turba, saboda barazanar da muke fuskanta iri daya ce."

Hakanan shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana farin cikin ta game da cewar, Rasha da Turai sun cimma matsaya guda wajen yin matsin lamba ga kasar Iran domin dakatar da shirin niukiliyar ta.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu