1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar shugaban ƙasar Fransa da shugabar gwamnatin Jamus

January 9, 2012

Shugaba Nicolas Sarkozy na tattaunana da Angela Merkel domin samin daidaito akan wasu manufofin tattalin arziki kafin taron ƙungiyar ƙasashen Tarrayar Turai

https://p.dw.com/p/13gVd
Merkel und Sarkozy treffen sich in Berlin
Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy da shugabar gwamnatin JamusHoto: dapd

Shugaban ƙasar Faransa Nicola Sarkozy na ganawa da shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel a birnin Berlin a ziyara aikin da ya soma.Shugabannin biyu waɗanda ke tattauna hanyoyin bunƙasa cigaban tattalin arziki a ƙasashen masu amfani da kuɗin euro, gabannin taron ƙungiyar EU da za a yi a ƙarshen wannan wata a birnin Brusels na ƙasar Beljium.

Na koƙarin samin daidaituwar baki akan wasu matakan na ƙara ƙarfafa tattalin arziki domin fuskantar ƙalubalen da ke a gaban Nahiyar.A ƙwanakin baya Shugaban ƙasar Faransa ya sanar da cewa zai ɓulo da wani sabon tsari na haraji akan hada hadar kuɗaɗe wanda ya ce ƙasar sa za ta yi aiki da shi, ko da sauran ƙasashen ba su amince ba ;Ko da shi ke shugabar gwamnatin jamus ta yin marhabin da shirin amma ta na fatan ganin kafin an a aiwatar da shi sauran ƙasashen ƙungiyar guda 27 sun amince da shi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasiru Awal