Ganawar shugaban Ghana dana Amurka a white house | Labarai | DW | 13.04.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar shugaban Ghana dana Amurka a white house

Ghana

Shugaba John Kufuor na Ghana ya mika godiyarsa ta musamman wa shugaba George W Bush na Amurka ,a dangane da tallafin dayake bawa kasarsa,sai dai yace kasashen Nahiyar Afrika zasu iya samun ingantuwan rayuwa ne ,da karin tallafi daga masu agaza musu.

Shugaban na Ghana yayi wannan furucin ne ayayin ganawarsa da shugaban Amurkan a wani rangadin aiki daya kai wannan kasa.A ganawar ta shugabannin biyu wadda ta gudana a fadar gwammnatin Amurka ta White house,shugaba Kufuor ,ya bayyana BBush da kasancewa shugaban dake taimakawa Afrika,wajen dogaro ga kai.Shugaban Ghanan yace tallafin da shugaba Bush yakeyi wajen yaki da cutar Aids da ilimin yara kanana,da inganta harkokin noma da kasuwanci,ya taimaka matuka gaya wa kasashen Afrika baki daya.To sai yace duk dacewa Ghana na cin moriyar shirin shekaru 5 ,na shigar da kayayyakin Afrika 6,400 cikin kasuwannin Amurka ba tare da haraji ba,kasarsa na bukatar karin tallafi.A nashi bangare shugaban Amurka ya taya takwaransa na Ghana murna,da kuma yabawa kokarinsa na kawo gaskiya da adalci acikin gwamnatin kasarsa,a hannu daya kuma da inganta tattalin arziki da zaman lafiyar alummarsa.Bush yace adangane da hakane aka zabi Ghana ta kasance daya daga cikin kasashen da zasu karbi tallafi na musamman daga Amurka.

 • Kwanan wata 13.04.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6y
 • Kwanan wata 13.04.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6y