1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Paparoma Benedict da jakadun kasashen musulmi

Zainab A MohammadSeptember 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5G

Paparoma Benedict na 16, ya gana da jakadun kasashen musulmi a fadarsa ta Galdolfo dake kusa da birnin Rome.Ayayin ganawar tasa da jakadun kasashen musulmi 22,da suka hadar da Iran da Turkiyya da Morocco,jagoran darikar katholikan ya jaddada cewa danganta tsakanin addinai,yana da matukar muhimmanci domin zamantakewa.Dayake jaddada huldodi tsakanin addinai daban daban ,paparoma Benedict yace hakan ne zai taimaka domin kyakkyawar makoma nan gaba.Bayan dan jawabin nasa na mintuna biyar,Paparoma yayi hannu dai bayan daya da dukkan jakadun kasashen muslmi 22 da suka halarci wannan ganawa.Makasudun wannan taron dai shine dinke barakar data kunno kai tsakanin musulunci da darikar katholikar,sakamakon kalamu marasa da,da paparoman yayi kann addinin musulunci a ranar 12 ga wannan wata.