Ganawar Obama da Sarkozy | Labarai | DW | 31.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar Obama da Sarkozy

Sarkozy ya kai ziyar a Wathington, inda suka tattauna da takwaransa na Amirka kan batutuwan siyasar duniya

default

Obama da Sarkozy

Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya kai ziyara a ƙasar Amirka, inda shi da shugaba Obama suka tattauna batutuwa da dama wadanda suka shafi siyasar duniya. Daga cikin abinda yafi ɗaukar hankalin ganawar Barack Obama da takwaransa na Faransa sunyi ƙira da a ƙaƙabawa ƙasar Iran takunkumi mai tsauri, a bisa manufar ta na mallakar makaman nukiliya. Shugabannin biyu sunyi ƙiranne a yayin jawabin haɗin gwiwa da suka yi wa manema labarai a fadar White house ta Amirka. Shugabannin suna masu cewa yanzu fa lokaci ya yi na ɗaukar mataki domin sun jima suna tun tuɓar ƙasashen China da Rasha da Jamus da Birtaniya. Obama ya ƙara da cewa shi da Sarkozy sun kuma tattauna batun kyautata tsarin kuɗi na duniya dama batun da ya shafi rikicin Palasɗinawa da Yahudawa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita:  Umaru Aliyu