1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar ministocin harkokin wajen Jamus da Afganistan

October 29, 2010

Jamus ta yi matsin lamba ga Afganistan da ta yaƙi cin hanci da rashawa.

https://p.dw.com/p/PuF4
Guido Westerwelle yayin wani taro akan AfganistanHoto: picture-alliance/dpa

Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle ya yi matsin lamba ga ƙasar Afganistan da ta yaƙi cin hanci da rashawa, ta kuma ba da horo ga dakarun tsaronta. Westerwelle ya yi wannan kira ne yayin ganawarsa da takwaransa na ƙasar ta Afganistan, Zalmay Rassoul a birnin Berlin na nan Jamus . Ya ce wajibi ne gwamnatin Afganistan ta tashi ta tsaya kan ƙafarta domin karɓar alhakin tsaron ƙasar a shekara mai zuwa. Ya kara da cewa kasar za ta fuskanci ƙalubale wajen tabbatar da bin doka da oda. A watan Nuwamba mai kamawa ne dai ake san ran cewa gamayyar ƙasashen duniya za ta nuna amincewarta da danƙa aikin tsaron ƙasar ta Afganistan ga gwamnatinta, yayin wani taron da ƙungiyar NATO za ta yi a birnin Lisbon na ƙasar Portugal.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Yahouza Sadissou Madobi